A yau da misalin ƙarfe 9 na dare zan miƙawa Abba mulkin Kano a Gidan Gwamnatin – Ganduje
Gwamnan Kano mai barin Gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai miƙa mulkin jihar ga zaɓaɓɓen gwamnan Kano mai jiran Gado, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a wannan Rana ta Lahadi 28 ga watan Mayu 2023, da misalin karfe 9 na dare a Gidan gwamnatin jihar, domin tafiya zuwa babban birnin tarayya Abuja, a ƙoƙarinsa na halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai mai barin Gado, kwamared Muhammad Garba, inda ya ce tuntuni kwamitin miƙa mulki ya gabatar da bayanai na Rahoton mulkin Ganduje ga kwamitin karɓar mulki, kamar yadda muka kalato daga Nasara Radio.