A yau Juma’a Kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci a kan kararar da dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, Atiku Abubakar da jam’iyyar tasa suka shigar ta neman soke takarar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a zaben da aka yi na 2023.
A karar da suka shigar suna neman kotun ta ayyana cewa takarar Tinubun da Shettima wadanda suka riga suka yi nasara a zaben ranar 25 ga watan Fabarairun 2023, karkashin jam’iyya mai mulki APC, cewa ba ta dace ba.
Masu korafin suna ikirarin cewa zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa, Tinubu ya saba wa sassa na 29(1), 33, 35, da kuma na 84(1)(2) na doka zabe ta kasar ta 2022.
A korafin suna cewa Shettima ya saba doka saboda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa da kuma kujerar majalisar dattawa ta Borno ta tsakiya a lokaci daya, kamar yadda BBC ta kalato.
A don haka ne wadanda suka shigar da karar suke neman kotun ta soke cancantar APC da Tinubu da Shettima daga takarar wadda suka riga suka yi ta zaben shugaban.
A hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya a Abuja da aka fara kai karar Justice Inyang Ekwo, ya yi, ya yi watsi da ita bisa dalilin cewa PDP ba ta da damar gabatar da korafin.