Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya zargi ‘yan siyasar da suka sha kayi a zaben 2023 da yunkurin jefa Najeriya cikin rikici, tare da yiwa kasar zagon kasa ta hanyar safarar abinci zuwa wasu kasashe domin tayar da farashin kayan abinci.
Mista Shettima, a ranar Talata a wani taro kan harkokin kula da dukiyar jama’a a Abuja, ya yi ikirarin cewa an kama manyan motoci 45 da ke safarar abinci daga kasarnan.
“Kimanin dare uku da suka gabata, an kama manyan motoci 45 na masara ana jigilar su zuwa kasashe makwabta,” in ji Mista Shettima. “Akwai a cikin wannan layin na Ilela, akwai hanyoyin fasa kwabri guda 32.”
Ya kuma kara da cewa, a dalilin haka, farashin masara ya fadi.
“Kuma a lokacin da aka kama wadannan kayan abinci, farashin masara ya fadi da N10,000. Ya sauko daga N60,000 zuwa N50,000. Don haka, akwai dakarun da ke da niyyar yi wa al’ummarmu zagon kasa, amma wannan lokaci ne da ya kamata mu hada kai zuwa wata kungiya daya,” in ji Mista Shettima.
Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa wasu ’yan siyasa na da burin su jefa Najeriya cikin rikici saboda gazawar da suka yi na kwace mulki a zaben da ya gabata.
“Suna da niyyar jefa kasar nan cikin wani hali na rashin zaman lafiya. Wadanda ba za su iya samun mulki ta hanyar akwatin zabe ba, maimakon su jira har zuwa 2027, sun yi matukar bakin ciki,” Mista Shettima ya jaddada.
Ya kara da cewa, “Dole ne mu sanya kasar nan ta yi aiki. Dole ne mu wuce siyasa. A yanzu muna fuskantar gwamnati. Abin bakin ciki, har yanzu wasu daga cikin ‘yan kasarmu suna cikin yanayin siyasa.
“Su ne masu aikata ta’addanci, suna ba da shawarar cewa Najeriya ta bi hanyar Lebanon. Najeriya za ta shawo kan guguwar.”
Mista Shettima bai ambaci sunayen ‘yan siyasar da ya zarga da jefa kasar nan cikin rudanin tattalin arziki da kuma yiwa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu zagon kasa ba.
Sai dai Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party da Peter Obi na jam’iyyar Labour, manyan ‘yan takara a babban zaben, sun ci gaba da nuna rashin amincewa da yadda Mista Tinubu ke tafiyar da tattalin arzikin kasarnan.