Al’ajabi

`Yan Najeriya sama da miliyan 20 ba su da aikin yi – NBS

Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar da rahoton cewa, ‘yan Najeriya sun kai adadin sama da miliyan 17.6 zuwa miliyan 20.9 na rubu’i na hudu na shekarar 2017 zuwa sulusin shekarar 2018 da ba su da ayyukan yi.

A wani rahoto da hukumar ta fitar na cewa, kididdigar jama’ar da aka fitar na wanda ba su da ayyukan yi na nuna cewa masu shekaru daga 15 zuwa 64 sun karu daga mutum miliyan 111.1 zuwa miliyan 115.5.

Rahoton ya kara da cewa, a cikin mutum miliyan 20.9 da ba su da ayyukan yi, mutum miliyan 8.77 ne suke neman aikin yin su na farko a kasar yayin da mutum miliyan 0.93 suka rasa ayyukan su, sai kuma mutum miliyan 11.1 da ke aiki kasa da sa’o’i 20.

Leave a Reply