Da alama zaben da za a yi a Najeriya a 2019 zai fi wadanda suka gabace shi ta fuskar rabuwar kawunan ‘yan Kannywood da ke mara wa mabambantan ‘yan takara baya. BBC ta rairayo bayanai a kan yadda abin yake.
Bayanai sun nuna cewa ba a taba samun adadin jaruman Kannywood da suka fito fili suka nuna alkiblarsu kamar a wannan lokaci ba.
Hasalima, tuni manyan jarumai irinsu Ali Nuhu da Adam A. Zango da Fati Washa suka ziyarci fadar shugaban kasa da ke Abuja inda suka bayyana shirinsu na mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya a yunkurin da yake yi na sake lashe zaben 2019.
Kazalika, jarumai irinsu Sani Danja da Fati Muhammad da Maryam Booth da Mika’ilu Bn Hassan Gidigo suka sha alwashin ganin tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ke takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, ya kai bantensa a zaben 2019.
A tattaunawar da na yi da shi, fitaccen mai ruwa da tsaki a Kannywood kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma’ila Naabba Afakallah, ya ce jaruman Kannywood suna da muhummiyar rawar da za su taka wajen ganin an samu shugabanci na gari a kasar.
Afakallah, wanda ke goyon bayan Shugaba Buhari, ya kara da cewa “muna da miliyoyin magoya baya wadanda ko ka so ko ka ki za su yi abin da muke so su yi saboda kaunar da suke yi wa masana’antar Kannywood: ciki kuwa har da zaben mutumin da muke so su zaba.”
A cewarsa, tsunduma cikin harkokin siyasa da taurarin fina-finan suka yi wata alama ce da ke nuna cewa sun daina nade hannayensu wurin sha’anin shugabanci ko da ba za a ba su ko sisi ba.
A nasa bangaren, fitaccen jarumi kuma furodusa, Falalu Dorayi, ya bayyana min cewa sabanin takwarorinsu na Amurka – wadanda ‘yan takarasu suka sha kaye a zaben Amurka – ‘yan wasan fina-finai Hausa suna da magoya bayan da ba sa kwance musu zane a kasuwa.
“Idan ka yi waiwaye za ka ga cewa a zaben 2015 mun yi kira ga magoya bayanmu su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi Muhammadu Buhari, kuma hakan aka yi.
“Don haka ina ganin yanzu ma za a kwata. Ba na shakkar amincin da ke tsakaninmu da magoya bayanmu,” in ji shi.
‘Wanda zai cika alkawari kawai ‘yan fim za su zaba’
Sai dai Mika’ilu Gidigo ya ce duk da yake taurarin fina-finan Kannywood na iya sauya alakar masu zabe amma masu kada kuri’a za su zabi mutumin da suke ganin yana da cika alkawari ne kawai.
“Ina so ka sani cewa al’uma daban-daban ce. Mu a Najeriya duk da goyon bayan da masu kallo suke yi mana ba za su zabi wanda bai cika musu alkawari ba.
“Idan ka dubi baya za ka ga cewa Shugaba Buhari ya yi alkawuran kawo sauye-sauye amma a zahiri adadin matasan da ba su da aiki yanzu ya fi na baya; mutanen da ke kwana da yunwa yanzu sun zarta na baya.
“Don haka za su bai wa masu kallonmu hujjoji ingantattu wadanda za su hana su sake zaben Shugaba Buhari a 2019,” In ji Gidigo.
A yayin da jarumai irin su Adam Zango, ke cewa suna goyon bayan Shugaba Buhari ne ba domin ya samu ko sisi ba, sai domin kawai ya gamsu da salon shugabancinsa, sannan Fati Muhammad, ke jaddada kiraye-kirayen da take yi cewa tana goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar ne saboda gwamnatin Buhari ta gaza kawo sauyin da ta yi alkawarin yi wa ‘yan kasar – masu sharhi sun yi wa batun kallon tsanaki.
Ra’ayin masu sharhi
Mallam Muhsin Ibrahim, wani masani kan harkokin Kannywood wanda kuma ke koyar da fina-finan a Jam’iar birnin Colonge na kasar Jamus, ya ce akwai yiwuwar jaruman Kannywood su yi tasiri kan masu kallonsu wajen zaben shugabanni saboda yanayin wayewa da sanin ‘yancin kai da ilimin Amurkawa daban yake da na ‘yan Najeriya.
“Eh, ina ganin jaruman fini-finan Hausa za su iya sauya tunanin masu kallonsu domin su zabi dan takarar da suke kauna.
“Kar ka manta matakin tunani da ilimin masu zabe a Amurka daban yake da na ‘yan Najeriya. Yawancin masu kallon ‘yan Kannywood suna yi musu soyayya tamkar bauta don haka za su iya yin duk abin da suka sa su.”
Sai dai Dr Daha Tijjani, wani Malami a jami’ar Limkokwing da ke Malaysia, wanda ya rubuta kundin digirin digirgir dinsa a kan tasirin da ‘yan fim suke yi wajen sauya tunanin al’uma, ya ce masu kallon fina-finain Kannywood, musamman matasa sun fi yarda da abin ake kira “sayen-na-gari mai-da-kudi-gida” ba wai abin da wani dan fim ya ce su yi ba.
A cewarsa, ko da ‘yan fim sun bukaci masu kallonsu su zabi mutum ba za su yi hakan ba sai idan suna ganin zai iya kawo sauyi a rayuwarsu.
Gani ga wane
Ganin yadda ‘yan fim a Najeriya suka shiga harkokin siyasa ta hanyar nuna goyon baya kara ga ‘yan takara, ga alama za a zuba ido don ganin ko taurarin fina-finan Kannywood za su iya sauya akalar zaben 2019, musamman idan aka yi la’akari da cewa takwarorinsu na Amurka, sun ji kunya, sakamakon yadda ‘yan takarar da suka mara wa baya suka gaza kai labari.
Alkaluman zaben tsakiyar wa’adin mulki da aka gudanar a Amurka a makon jiya sun suna cewa taurarin fina-finai da mawaka ba sa iya yin tasiri wurin ganin ‘yan takara sun ci zabe.
Bayanai da dama sun nuna yadda duk da miliyoyin mabiyan da wadannan taurari ke da su, ba su iya taimakawa ‘yan takarar da suka mara wa baya wurin cin zabe ba.
Misali, har zuwa ranar zabe, Beyonce ta fito fili ta goyi bayan dan jam’iyyar Democrat Beto O’Rourke a zaben majalisar dattawan jihar Texas – sai dai sanata mai-ci Ted Cruz ya kayar da shi.
Kazalika, Rihanna ta yi kira ga magoya bayanta a Florida su zabi Andrew Gillum a matsayin gwamna, amma ya sha kashi a hannun dan Republican Ron deSantis.
Haka kuma dan takarar sanatan da Taylor Swift ta mara wa baya a Tennessee ya sha kaye a hannun ‘yar Republican mai ci, Marsha Blackburn.
Wannan rashin tasiri na taurarin fina-finai da mawaka ya sa masu nazari kan harkokin fina-finan Hausa na Kannywood na ganin ba za a yi saurin yanke hukunci kan irin tasirin da ‘yan wasan na Hausa za su yi a zaben 2019 ba sai bayan zaben.