Wasu ’yan bindiga sun kai hari a kauyaku tara na Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna inda suka kashe sama da mutum 50, sannan suka sace wasu da dama.
Wani mazunin yakin da Aminiya, ta tattauna da shi kuma ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya auku ne a daren Alhamis zuwa wayewar garin Juma’a.
Ganau din ya ce tun da misalin karfe 7:00 na yamma ne aka fara ganin bakin a kan babura dauke da bindigu, kuma an yi kokarin samar da jami’an tsaro.
Kauyakun da ’yan bindiga suka kutsa sune, auguwar Kaya Fatika, Barebari Dillale, Zangon Tama, Anguwar Bakko, Gidan Alhajin Kida da kauyan Kadanya da Doromi, duk a cikin karamar hukumar ta Giwa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.