A ci gaba da yakin da ake yi da ƴan fashin jeji, dakarun rundunar sojojin Najeriya na ‘Operation Whirl Punch’ sun kashe ‘yan bindiga a wata maɓoyarsu a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A cewar wani rahoto da rundunar ta fitar, sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri sun kai wani mummunan sumame na yaƙi a yankin Abasiya-Amale da ke gabashin Polewire a Ƙaramar Hukumar Kachia, inda suka fafata da ƴan bindigar.
A wannan kazamin fadan, sojojin sun yi galaba a kan ƴan bindigar, inda daga bisani suka lalata maboyarsu.
Har yanzu dai sojoji na ci gaba da kutsawa da mamaye a yankin a daidai lokacin da aka samu wannan rahoton, yayin da aka kwaso gawarwakin ‘yan fashin guda biyu.
An kuma kwato kayayyaki kamar haka: bindigar AK-47 guda daya; gidan saka harsashi guda biyu dauke da harsashi 38 da; wayar salula daya.
A cewar sanarwar da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya fitar, akwai kwakkwarar alamu da ke nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun tsere da raunukan da ke barazana da rayuwarsu, kuma watakila suna neman agajin gaggawa a yankin baki daya.
“Don haka, an gargadin mutanen yankin da su guji ba da duk wani irin su taimako, maimakon haka su kai rahoton irin wadannan lambobi: 09034000060.
0817018999.
Za a sanar da jama’a kan ci gaba da a ke samu,” inji shi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.