A daidai lokacin da siyasa ke kara karatowa, harkoki a kafofin sadarwa na zamani na kara zafi. Ba a bar jaruman fina-finan Hausa ba a wannan bangare domin tuni suka fara amfani da yawan mabiyansu wajen kara tallata ’yan siyasar da suke kauna, tare da baje kolinsu ganin cewa sun fi da yawa daga cikin ’yan siyasar kasar yawan mabiya a shafukan na sada zumunta.
Matsalolin da yawanci jaruman suke fama da su, sun hada da yadda wadansu suke amfani da sunansu na bogi a kafofin sadarwar ba tare da saninsu ba.
Yadda ake gane sahihin shafi a kafar sadarwa akwai alamar tantancewa, inda za a ga alamar maki
Jarumi Nuhu Abdullahi ya shaida wa kafar labarai ta Premium Times a kwanakin baya cewa, “Duk da cewa kafar Facebook kafa ce mai matukar amfani, akwai wadanda suke amfani da sunanmu na bogi. Don haka ne wadansu daga cikinmu suke kaurace wa Facebook. Mun fi son kafar Instagram domin tana da saukin mu’amala.”
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna yadda masana’antar Kannywood ta rabu biyu kan ’yan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari da na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Binciken ya nuna ’yan fim din da ke goyon bayan Atiku da suka hada da Mika’il bin Hassan (Gidigo) da Sani Danja da Fati Muhammad da Zaharaddeen Sani da Usman Mu’azu da Ummi Zee-Zee da Salisu Mu’azu da Mustapha Naburuska da mawaki Abubakar Sani da sauransu.
Wadanda kuma ke goyon bayan Buhari sun hada da mawaki Dauda Kahutu Rarara da Yusuf Haruna (Baban Chinedu) da Adam A. Zango da Bello Muhammad Bello da Fati Nijar da Abdul Amart (Mai Kwashewa) da Halima Atete da Jamila Nagudu da Aminu Ladan Abubakar (ALA) da Rukayya Dawayya da sauransu.
Da yake jawabi a lokacin da ’yan fim suka kai wa Atiku Abubakar ziyara, Aminu Shareef Momoh ya bayyana masa cewa suna da dimbin mabiya a kafafen sadarwa na zamani a daidaikun shafukansu, da shafukan da suka bude na tallata shi a matsayin dan takara.
Baya ga harkokin siyasa da suke tattaunawa, yawancin jaruman ana iya samunsu ne a irin wadannan kafofin. Don haka ne Aminiya ta rairayo yadda jaruman suke amfani da kafofin sadarwar da yawan mabiyansu.
1. Ali Nuhu
Ali Nuhu mai Kamfanin FKD, wanda ake yi wa lakabi da Sarki shi ke biye da Rahama Sadau, inda yake da sama da mabiyu dubu 800 a shafinsa mai suna @realalinuhu da aka tantance.
Ali Nuhu fitaccen jarumi da ya dade yana taka rawa a fina-finan Hausa da na Kudu. Jarumi, kuma darakta ne kuma shi ne ya yi sanadiyar shigo da wadansu daga cikin manyan ’yan fim, wanda hakan ya sa suke girmama shi matuka.
A bangaren Tiwita kuma, Ali Nuhu ya fi yawan mabiya, inda yake da sama da mabiya dubu 21 a shafinsa mai suna @alinuhu da aka tantance.
Haka ma a Facebook Ali Nuhu ya fi kowa yawan mabiya a cikin ’yan fim, domin ya fi sauran jaruman mu’amala da kafar. Yana da mabiya sama da miliyan daya a shafinsa da aka tantance.
2. Rahama Sadau
Rahama Sadau tana daya daga cikin matan da tauraronsu ke haskawa a masana’antar Kannywood a yanzu. Tana taka rawa a fina-finan Hausa da na Kudu na Inglishi. Ta yi fice sosai a Instagram, inda take sanya hotuna da kananan faifan bidiyo.
Rahama Sadau ita ce kan gaba a mabiya a kafar Instagram daga cikin dukan jaruman Kannywood. Rahama tana da sama da mabiya miliyan daya a shafinta na Instagram mai suna @rahamasadau da aka tantance.
A shafin Tiwita kuma, Rahama tana da mabiya sama da dubu 174 a shafinta mai suna @Rahama_sadau da aka tantance. A tiwita takan tattauna da magoya bayanta kai- tsaye inda a kwanakin baya ta sanya wata muhawara a kan wanda ya kamata ta zaba, wanda ya jawo zazzafar muhawara.
A facebook ma an tantance Rahama, kuma tana da mabiya sama da dubu 600.
3. Adam A Zango
Adam A. Zango wanda ake yi wa lakabi da Yarima, yana da mabiya sama da dubu 700 a shafinsa na Instagram mai suna @adam_a_zango da aka tantance.
A Tiwita, Zango yana da sama da mabiya dubu 63 a shafinsa mai suna @princezango da aka tantance, sannan yana da sama da mabiya dubu 24 a Facebook.
Zango mawaki ne na zamani wanda ya shige gaba wajen zamanantar da kida da waka a masana’antar, kuma darakta.
4. Nafisat Abdullahi
Nafisat Abdullahi, wadda ake kira Nafisa Sai Wata-Rana ko kuma ’Ya Daga Allah, fitacciyar jaruma ce da ke da dimbin masoya. Yanzu haka tana da sama da mabiya dubu 700 a shafinta na Instagram mai suna @Nafeesat_official da aka tantance.
A Tiwita tana da mabiya sama da dubu 19 a shafinta mai suna @NafisatOfficial. Aminiya ta gano cewa da tana da wani shafin mai mabiya da yawa da suka dara na wannan shafin, kafin daga baya ta canja. Sai a Facebook da take da sama da mabiya dubu 52.
Nafisa jaruma ce kuma mai shirya fina-finai, inda yanzu haka masoya suke shaukin fara kallon fim dinta na ‘Yaki A Soyayya.’
5. Hadiza Gabon
Hadiza Aliyu Gabon, jaruma wadda ta yi fice musamman a fina-finan barkwanci da na soyayya, tana da mabiya sama da dubu 900 a shafinta na Instagram mai suna @adizatou da aka tantance.
A shafin Tiwita, Gabon na da mabiya sama da dubu 13 a shafinta mai suna @AdizatouGabon da aka tantance, sannan tana da sama da mabiya dubu 400 a Facebook.
Sauran ’yan fim da suke amfani da kafar sadarwa sosai sun hada da mawaki Umar Shareef da yake da mabiya sama da dubu 431 a shafinsa na Instagram mai suna @umarshareef da aka tantance, Ummi Ibrahim Zeezee tana da mabiya sama da dubu 316 a shafinta mai suna ummizeezee. Sai Hafsat Idris da take da mabiya sama da dubu 633 a shafinta mai suna @official_hafsatidris a Instagram.
Shi ma mai shirya fina-finai Abubakar Bashir Maishadda, wanda yanzu haka fina-finansa suke taka rawa sosai wajen nishadantarwa da fadakarwa yana da mabiya sama da dubu 139 a shafinsa na Instagram mai suna @realabmaishadda
Darakta Aminu Saira yana da sama da mabiya dubu 64 a shafinsa mai suna @AminuSaira da aka tantance a Tiwita.
Tuni dai wadansu daga cikin jaruman suka fara amfani da shafukan nasu wajen tallata ’yan siyasar da suke so mutane su zaba.