BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Tsofaffin dalibai sun yaba da rushe gine-gine a Kano

Kungiyar tsofaffin daliban makarantar GSS Goron Dutse ta yabawa gwambatin Kano bisa matakin da ta dauka na rushe shagunan da gine-ginen da aka yi a harabar makarantar da kewayen ta wanda gwamnatin data gabata ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta gudanar.
Kafin wannan lokaci, tun a baya, Kungiyar tayi Allah-wadai da yadda gwamnatin da ta gabata ake zargin ta yi “watandar” harabar makarantar ga wasu tsirarun marasa kishin ilimi.
Kungiyar ta kasa ta bayyana goyan bayan ta ga matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauka na rushe gine-ginen da akayi a makarantar ba bisa ka’ida ba ta bakin Babban Jami’in hulda da Jama’a na daya Comrade Salisu Ismail Kabuga.
“Mun dade muna fatan Allah ya kawo gwamnatin da zata kubutar da makarantun Ya’yan talakawa wadanda gwamnatin data gabata ta hada baki da Yan kasuwa marasa kishin ilimi wajen gididdiba su”. In ji Æ™ungiyar, a wata sanarwa da kakakin ta, Salisu Kabuga ya rabawa manema labarai.
“A lokacin da gwamnatin Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta fara sayar wa Yan kasuwa harabar makarantar ba irin kokari da kungiyar bata yi ba domin nusar da gwamnati amma ta toshe kunnen ta,” kamar yadda muka kalato daga Daily Nigerian Hausa.
Kakakin kungiyar na kasa ya kara da cewa, “Gwamnatin data gabata ta yaudari kungiyoyin dalibai wajen siyar da kewayen makarantun da abin ya shafa domin kara inganta yanayin da makarantun ke ciki, amma babu abinda ya sauya sai ma kara tabarbarewa da sukayi yadda hatta kujerun zaman dalibai da Alli ya gagari makarantun”.
Comrade Kabuga ya kuma bukaci gwamnatin Jiha data kara himma a kudurin data dauka na inganta sha’anin ilimi ta hanyar dawowa da makarantun iyakokin su da aka salwantar a baya da kuma samar da dukkaninin abubuwan da ake bukata a makarantun na sha’anin koyo da koyarwa. Inda ya baiwa gwamnatin tabbacin samun hadin kai da goyan bayan kungiyoyin tsofaffin daliban makarantun jihar Kano wajen cimma nasarar abinda ta sanya a gaba.

Leave a Reply