A ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2020 ne Kotun Koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Abba Kabir Yusuf, ya shigar domin kalubalantar nasarar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan jihar.
Wannan shi ne karo na uku da Abba Kabir, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya shigar da kara yana kalubalantar nasarar ta Ganduje.
Wannan hukuncin kotun na nufin Ganduje zai ci gaba da zama kan kujerar mulki zuwa karshen wa’adinsa a zangon mulkinsa na biyu, baya ga zangon farko na shekara hudu da ya yi daga shekarar 2015 zuwa 2019.
Shin wane ne Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje? BBC ta yi nazari kan tarihinsa, kamar yadda BBC ta tattaro:
Rayuwarsa
An haifi Abdullahi Umar a kauyen Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano a 1949.
Ya fara karatun Kur’ani da Islamiyya a kauyensa inda ya samu ilimin addini.
Daga nan kuma ya shiga makarantar firamare ta Dawakin Tofa daga 1956 zuwa 1963.
Ganduje ya fara makarantar sakandaren Birnin Kudu daga 1964 kuma ya kammala ta a 1968.
Bayan nan, Ganduje ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano tsakanin 1969 zuwa 1972 inda ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.
Ya kammala karatun jami’a a fannin ilimi cikin shekarar 1975.
A 1979 ne kuma ya kammala digirinsa na biyu daga Jami’ar Bayero ta Kano sannan ya kara komawa Ahmadu Bello daga 1984 zuwa 1985 don karantar ilimin tafiyar da gwamnati.
A shekarar 1993 ne ya samu digirin-digirgir daga Jami’ar Ibadan.
Siyasa
Ganduje ya shiga jam’iyyar NPN a janhuriyya ta biyu sannan ya zama mataimakin sakatare na jihar Kano daga 1979 zuwa 1980.
Ya tsaya takarar wakiltar Kano a zauren majalisar wakilai a 1979 a jam’iyyar NPN amma bai yi nasara a zaben ba.
A shekarar 1998 ya shiga jam’iyyar PDP inda ya nemi jam’iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna, amma bai yi nasara ba bayan da PDPn ta tsayar da Rabi’u Musa Kwankwaso.
An zabi Ganduje a matsayin mataimakin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso tsakanin 1999 da 2003. Baya ga haka, an nada shi a matsayin kwamishinan kananan hukumomi.
Daga shekarar 2003 zuwa 2007, ya rike mukamin mai bai wa ministan tsaro na Najeriya, wato Rabi’u Kwankwaso, shawara ta musamman a bangaren siyasa.
An zabi Ganduje a matsayin shugaban kwalejin fasaha a Ado Ekiti a 2008 daga nan kuma aka nada shi a matsayin babban sakataren Hukumar Kula da Tafkin Chadi da ke Ndjamena.
Ya kuma kasance daga cikin wadanda suka halarci taron yi wa tsarin siyasa a Najeriya garambawul a 2006.
Kwankwaso da Ganduje sun kuma yi rashin nasara a zaben da suka nemi ta-zarce inda Malam Ibrahim Shekarau ya samu nasara.
An sake zabar Kwankwaso da Ganduje ranar 27 ga watan Afrilun 2011 inda aka rantsar da su ranar 29 ga Mayun 2011 domin karasa zangon mulkinsu na biyu.
Gwamnan Kano da rikicinsa da Kwankwaso
A ranar 28 ga watan Nuwamban 2014 Kwankwaso ya tsayar da Ganduje a matsayin wanda zai yi takarar gwaman jihar Kano a 2015.
Ya kuma yi nasara kan abokin adawarsa a babban zaben, Malam Salihu Sagir Takai da kuri’a 1,546,434 yayin da Takai ya samu kuri’a 509,726 a zaben 11 ga watan Afrilun 2015.
Sai dai ba a jima da zamansa gwamna ba sai aka fara jin kansu da Sanata Kwankwaso, inda a shekarar 2016 rikicinsu ya ta’azzara.
Mutanen biyu sun daina ko ga-maciji da juna tun bayan zaben shekarar 2015, wanda tsohon Gwamna Kwankwaso ya goyi bayan mataimakin nasa wurin lashewa.
Sai dai bangaren Ganduje na cewa yunkurin tsoma bakin Kwankwaso cikin sha’anin gwamnatinsu ne ya raba kawunan tsofaffin aminan biyu, zargin da bangaren Kwankwaso ya sha musantawa.
A shekarar 2018 ne wasu fitattun ‘yan Najeriya suka soma shiga tsakani a rigimar da ke tsakanin mutanen biyu, ciki har da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC a lokacin.
Zarge-zargen cin hanci
A watan Oktobar 2018 ne wasu jerin bidiyo suka bazu a shafukan sada zumunta wadanda ke nuna Ganduje na karbar cin hanci daga hannun wasu ‘yan kwangila, bayan da wata jarida a intanet ta Daily Nigerian ta yi bankadar.
Bidiyon wadanda suka bayyana gabanin gudanar da zaben 2019 sun yamutsa hazo a Kano, amma Ganduje ya ce zarge-zargen ba su da tushe balle makama.
A cewarsa, wasu ‘yan hamayya ne kawai suke kokarin bata masa suna don su samu nasarar cin zaben 2019.
A watan Oktoban 2018 majalisar jihar Kano ta fara bincikar lamarin, amma a watan Disambar shekarar sai kotu ta yanke hukuncin dakatar da majalisar daga binciken.
Ko wane kalubale ke gaban Ganduje a zango na biyu?
Sai dai duk da wadannan abubuwa da suka yi ta faruwa, Gwamna Ganduje ya samu damar lashe zaben gwaman a karo na biyu da aka gudanar a watan Maris din 2019, duk da zarge-zargen tafka magudi da cin zarafin masu zabe lokacin zaben, wadanda kungiyoyi irin su Tarayya Turai da sauran kungiyoyin sa ido na kasa da kasa suka bayar da rahoto.
Bayan nasarar da Ganduje ya samu a zaben, BBC ta yi nazari kan irin kalubalen da ke gabansa inda kuma masana suka lissafa kalubale biyar.
- Rarrabuwar kan al’ummar jihar
- Harkar Tsaro
- Harkar Ilimi
- Inganta rayuwar al’umma
- Mutanen da zai yi aiki da su
Iyali
Gwamna Ganduje yana da mata daya Hajiya Hafsat Ganduje da aka fi sani da Gwaggo.
Yana kuma da ‘ya’ya da dama daga cikinsu akwai Habiba da Amina da Fatima da kuma Abba.