Gwamnatin tarayyan Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tace ta magance mafi munin matsalar tsaro a ƙasar nan. Ta ce yan ta’adda na kokarin guduwa amma ba zasu tsira ba.
Kafar Legit ta ruwaito daga The Nation cewa gwamnatin tarayya na cewa ‘yan ta’adda, yan fashin daji da duk wasu gungun yan tada kayar baya basu da mafaka a faɗin ƙasar.
Ta ƙara da cewa ‘yan Najeriya ka iya ganin ‘yan tsirarun Kes ɗin matsalar tsaro nan da can amma ba zai yi muni kamar yadda ta faru a baya ba. An bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na Ministoci huɗu tare da babban Hafsan tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor. Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng! Ministocin sun haɗa da Alhaji Lai Muhammed (Yaɗa labarai), Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya (Tsaro), Rauf Aregbesola (Cikin gida) da Mohammed Maigari Dingyadi (Harkokin yan sanda). Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed yace: “Kamar yadda kowa ya sani, batun tsaro ya zama abinda muka fi tattauna wa a kai a baya-bayan nan, yan ta’adda, yan fashi da masu garkuwa a arewa maso Gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.” “Rikicin yan aware da ɓarayin mai a kudu-kudu da kudu-gabas, sai kuma yan asiri, fashi da makami a kudu maso yamma. Yau mun zo mu faɗa muku, duk da bamu kai gaci ba, Sojoji da sauran jami’ai na samun nasarar dawo da zaman lafiya a hankali.”
An bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na Ministoci huɗu tare da babban Hafsan tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor. Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng! Ministocin sun haɗa da Alhaji Lai Muhammed (Yaɗa labarai), Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya (Tsaro), Rauf Aregbesola (Cikin gida) da Mohammed Maigari Dingyadi (Harkokin yan sanda). Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed yace: “Kamar yadda kowa ya sani, batun tsaro ya zama abinda muka fi tattauna wa a kai a baya-bayan nan, yan ta’adda, yan fashi da masu garkuwa a arewa maso Gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.” “Rikicin yan aware da ɓarayin mai a kudu-kudu da kudu-gabas, sai kuma yan asiri, fashi da makami a kudu maso yamma. Yau mun zo mu faɗa muku, duk da bamu kai gaci ba, Sojoji da sauran jami’ai na samun nasarar dawo da zaman lafiya a hankali.”
Akwai sauran yaƙi – Lai Muhammed Ministan ya ƙara da cewa Sojoji da sauran dakarun hukumomin tsaro sun ci nasara kuma suna kan samun nasara a yaƙin da suke da ayyukan ta’addanci sassan Najeriya. “Saboda haka ba muna nufin yaƙi ya ƙare ba, abinda muke kokarin cewa shi ne Sojojin mu da jami’an sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar ɗauke mafi munin ƙalubalen da muke fama, kuma hakan na nufin mafi munin ya ƙare.” “A halin yanzu mun tasa yan ta’adda, yan fashin daji da sauran masu taimaka musu a gaba, kuma ba zamu sassauta musu ba har sai mun ƙarar da su baki ɗaya.”