Wata tawagar rundunar sojin Najeriya ƙarƙashin Manjo Janar Taoreed Lagbaja hadin gwiwa da wasu jami’an tsaro sun fatattaki ƴan bindiga a wasu yankunan jihar Kaduna, mai fama da ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga.
Rundunar ta kai samame kan yankunan Buruku da Udawa da Manini da Birnin Gwari da Doka da Maganda da Kuyello da Dogon Dawa jiya Litinin.
Yayin ɓata-kashin, sojojin sun ci ƙarfin ƴan bindigar ta hanyar amfani da manyan makamai wajen halaka ɗaya daga cikinsu, wasu uku kuma aka cafke su da ransu sai kuma wasunsu da suka tsere da raunuka.
Sanarwar da kakakin rundunar Kanar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce sojojin sun kuma gano bindiga ƙirar AK47 da alburusai da baburan hawa 18.
Rundunar sojin ta kuma nemi hadin kan al’umma wajen bankado mutanen da aka gansu da harbin bindiga tare da kjai rahoto ga hukumomin tsaro kamar yadda muka kalato daga BBC.