A wani rahoto na BBC Hausa ya tabbata cewa wani soja ne ya harbe shahararren Malamin nan Gwani Makarancin Kura’ani mai girma mai suna Gwani Aisami Gashuwa, kuma sojan ya kasheshi ne domin ya sace motar malamin ya kuma sayar.
BBC Hausa ta rawaito cewa Shaihin Malamin ya dawo ne daga Kano akan hanyarsa ta zuwa garin Gashuwa a jihar Yobe inda ya haɗu da sojan mai suna Kofur John wanda baya sanye da kayan soji a lokacin, sai ya nemi malamin ya rage masa hanya, inda ya faɗawa Malamin cewa shi soji ne, shaihin Malamin ya ɗauke shi a motarsa ya kuma rage masa hanya, sai dai a lokacin da Malamin ya buƙaci kama ruwa ya sauka zai kama ruwa sai sojan ya fiddo da bindigar AK47 cikin kayansa ya harbe Malamin.
Bayan sojan ya kashe malamin sai ya kira abokinsa mai suna Lans Kofur Gidiyon domin yazo ya taimaka masa su tafi da motar Malamin, sai dai dubunsu ta cika ne bayan da al’ummar yankin suka zata hatsari ne ga abku inda suka ankarar da ‘yan sanda, zuwan ‘yan sanda wajen sai kuma tarar da sojojin suna ƙoƙarin tafiya da motar Shaihin Malamin nan take suka yi masu ƙofar rago suka kame su a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa.
Sojan da ya kashe Malamin, Kofur John ne ya bai wa ‘yan sanda labarin yadda ya kashe malamin.
Zuwa yanzu sojojin biyu da suka kashe shehin malamin suna hannun ‘yan sanda.