BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Shin Rarara ya hau jirgin Shugaban Kasa?

Jaafar Jaafar

Jirgin haya ko “jirgin shugaban kasa”?

A binkicen da na yi, na gano cewa jirgin da ya dauko mashahurin makadin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara ba ya cikin rukunan jiragen fadar shugaban kasa, wato ‘Presidential Fleet’.

A da tabbas jirgin yana ciki, amma daga baya da aka siyo sabo, sai aka ba wa Nigerian Air Force (NAF) su yi abinda ya jibanci sha’anin aikinsu da shi.

Wani da ya san bayanai akan jirgin ya tabbatar min da cewa NAF haya/shata ta ke ba wa jam’ian gwamnati jirgin, kuma ko mutum ba jami’in gwamnati ba ne, ya kan yi kamun kafa da wasu jam’ian a ba shi shata. Jami’n ya ce shi jirgi ba’a son ajiye shi gungurun ba’a hawa. Wannan ya sa NAF ta ke wasa injin jirgin ta hanyar sahalewa gwamnoni da ministoci dss amfani da shi a farashi mai rahusa.

Bambancin wannan jirgi da ragowar jiragen shata shi ne, ya fi na yan kasuwa araha kuma ‘yan siyasa na kwalisa da burga da shi don nuna cewa su na da daurin gindi a fadar shugaban kasa. A wasu lokutan kuma yan siyasa na amfani da jirgin don cewa shugaban kasa na bayansu.

Tunda doka ba ta ba wa NAF izinin ba da jirage haya ko shata ba, wannan ya sa jam’ian gwamnati ke biyan naira miliyan uku don a sha mai, da kuma dan alawus da za’a sha ruwa a tauna goro. Wato idan da jirgin yan kasuwa ne, sai mutum ya biya akalla miliyan bakwai zuwa sama don yin shata.

Jaafar Jaafar ya wallafa a shafinsa na Facebook

Leave a Reply