BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Na hakura da takarar Sanata-Ahmed Lawan

Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmed Lawan ya ce ya karbi hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya ce ba shi ne halattaccen dan takarar majalisar dattijai na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa ba.

Matakin na zuwa ne kwana guda bayan hukuncin kotun da ke zamanta a birnin Damaturu game da halattaccen dan takarar sanata a jam’iyyar APC daga mazabar Yobe ta Arewa.

Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa nasada zumunta, Sanata Ahmed Lawan ya ce bayan tuntubar abokan harkar siyasa da magoya baya da abokan arziki, “Na yanke shawara ba zan daukaka kara a kan hukuncin ba. Na karbi kaddara,” kamar yadda BBC ta kalato daga sanarwar.

Sanarwar ta kunshi wani bayani mai alamta yin ban kwana, inda ya yi godiya ga shugabannin siyasar jiharsa ta Yobe da ma al’ummar mazabarsa da ya wakilta tsawon shekaru a majalisun tarayyar Najeriya.

Leave a Reply