A yayin da mayaƙan Boko Haram da suka tuba kuma suka miƙa wuya ga gwamnati tare da ajiye makamansu da kuma yin watsi da ayyukan ta’addanci ke ci gaba da samun karɓuwa a hannun al’ummomi, akwai matukar damuwa da matan cikinsu suka ce suna fuskanta ta wahalar samun mazajen aure.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani bincike da aka yi ya nuna cewa, ko da yake ‘yan ta’addar da suka tuba suna zaune a cikin al’ummominsu daban-daban, matan da ke cikinsu sun koka da cewa tun dawowarsu, babu wani na miji da ya fito neman aurensu, kasancewar mazajen suna guje musu kamar annoba.
Bayanai daga hukumomi sun nuna cewa adadin ƴan boko haram ɗin da suka miƙa wuya da iyalansu ya kai 162,000, amma babu irin wadannan bayanan da suka nuna adadin waɗanda suka sake aure, ko kuma zawarawa a cikinsu.
Wasu daga cikin shugabannin al’ummomin sun koka da yadda mazajensu ke fargabar shiga kowace irin salon soyayya da ƴan matan boko haram din duk da cewa sun miƙa wuya da kuma yadda wasu daga cikin matan ke bayyana sha’awarsu ta neman aure.