Muhimmancin Kirsimeti Da Sabuwar Shekara
Wurin Karatu: Matta 1:21-23 :–
“Za ta haifi da; kuma za ka kira sunansa Yesu; gama shi ne za ya ceci mutanensa daga zunubansu. Dukan wannan fa ya zama domin a cika a in da Ubangiji ya fadi ta baki annabi, cewa, duba, budurwa za ta yi juna biyu, za ta haifi da, za a kira sunansa Immanuel; watau, Allah tare da mu.”
Waxannan ayoyin, cikon annabcin Annabawa akan zuwa Yesu Almasihu domin ceto masu zunubi.
Littafi Maitsarki na tabbatar mana kyawawan sunayen Yesu masu ma’ana kamar haka;
- Yesu – Gama shi ne za ya ceci mutanensa daga zunubansu.
- Immanuel – Watau, Allah tare da mu.
Da ma’anar sunayen Yesu masu girma da daraja, muna iya san Mahimmancin Krisimas tare da dallilin Allah Ubangiji Allah ya aiko shi a duniya.
A takaice ga Mahimmancin Krisimas:
- Domin a tabatar da kamnar Allah Ubangiji ga dukan duniya ko ga Bil Adama baicin zunubin su. Watau Allah ya aiko da Yesu Almasihu a duniya domin Allah na kamnar duniya ne (Yohanna 3:16).
- Domin Kiristoci su tabbatar wa duniya kamnar Allah ta wurin Yesu Almasihu.
- Krisimas shaida ne cewa Yesu Almasihu ya zo duniya domin ceton duniya.
- Mahimmancin Krisimas domin a kyautata zamantakewa
- Mahimmancin Krisimas shi ne kara dankon zumunci da karfafa juna a cikin bangaskiya.
- Domin girmama da daraja Yesu Almasihu.
- Krisimas wata shaida ne fa da cewa ceto ta shigo duniya
- Mahimmancin Krisimas shi ne salama ta shigo duniya.
- Mahimmancin Krisimas domin sasanci tsakanin mutum da Allah da kuma sasanci ne tsakanin mutum da mutum.
- Mahimmancin Krisimas na tattare alherin Ubangiji Allah ga Bil Adama.
- Mahimmancin Krisimas domin shaidan Bishara salama fa ceto.