Dauda LawalGwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa nadin da aka yi wa magajinsa Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro bai samar wa jihar komai ba. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani shiri kai tsaye a gidan Talabijin na Channels Television a Yau Talata.
Da aka tambaye shi ko aikin Matawalle a matsayin Karamin Ministan Tsaro ya taimaka wajen yakar ‘yan bindiga da ke addabar Zamfara, Lawal ya ce, “Abin sha’awa ne a kullum idan wannan batu na Ministan Tsaro ya fito. Eh, shi ne karamin ministan tsaro, amma wane amfani gare mu? Makonni kadan da suka gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari garinsu tare da kashe mutane da dama.
Me yayi akai? Muna da Ministan Tsaro, amma baya amfanar da Jihar Zamfara komai.
Bello Matawalle ya yi gwamnan Zamfara daga watan Mayun 2019 zuwa Mayu 2023 kuma ya kasance dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben Gwamna na 2023.
Dauda Lawal wanda ke wakiltar jam’iyyar PDP ya doke Matawalle a zaben.
Bayan kayen da ya sha, an nada Matawalle a majalisar ministocin shugaba Bola Tinubu a watan Agustan 2023 a matsayin karamin ministan tsaro.