Ɗan takarar shugabancin kasa a inuwar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa shugabannin ƙungiyar Kiristoci ta kasa CAN cewa ba zai saka batun addini a mulkinsa ba, muddin ya yi nasara a zaɓen 2023.
Tinubu ya ce shi Musulmi ne sai dai matarsa da ‘ya’yansa duk Kiristoci ne.
Tsohon gwamnan na Legas ya faɗawa CAN wadannan maganganun ne a Abuja a kokarin nuna musu cewa yana tare da su kuma bambanci addini ba zai yi tasiri a shugabancinsa ba.
Batun zaɓin da Tinubu ya yi na Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ya ja hankali da haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan kasar musamman Kiristoci da ke ganin anyi musu rashin adalci.
Sai dai Tinubu ya ce shi burinsa shi ne kafa gwamnati mai nagarta ba wai bisa addini ko kabilanci ko wani abin da mutum ya yarda da shi ba, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Dan takarar ya ce shi mutum ne da ke neman kawo sauyi a Najeriya, shi yasa yake neman haɗin-kan kowa ba tare da nuna bambamci na addini ba, wajen kai kasar ga nasara.
Tinubu ya tausasa zuciyar shugabanni CAN tare da musu alkawarin cewa za su more a mulkinsa.