Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

Matar da mijinta ya kulle na wata takwas ta rasu

Matar nan ‘yar Jihar Yobe da ake zargin mijinta ya kulleta a daki a na tsawon wata takwas a Jihar Kano ta .

A makon juya ne mahaifiyarta ta ziyarce ta bayan ta kwashe watanni ba ta samun yarinyarta a waya, inda a duk lokacin da ta kira yake ce mata ba ta kusa.

Hakan ya sa ta musu ziyarar ba-zata, inda ta same ta cikin mawuyacin hali a gidan mijin nata wanda ya kulle ta, ya kuma barta cikin yunwa.

Labarin matar ya karade kafafen yada labarai ne bayan mahaifiyar ta kai ta asibiti, inda ta zargin mijin da yin asiri da ‘yarta.

Sai dai bayan kwanaki a asibiti, yanzu matar ta rasu.

Tuni an kama mijin yana hannun ‘yan sanda.

Leave a Reply