Majalisar Wakilai ta yi kira ga Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola da ya matsa wa ’yan kwangila su kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna nan da kankanin lokaci.
‘Yan majalisar na son kamfanin Julius Berger da ke aikin kwangilar da ya dawo ya ci gaba da aikin hanyar tare da kammala hanyar Jere zuwa Kaduna ba tare da bata lokaci ba.
Bukatar yin hakan ta taso ne a sakamakon amincewa da wani kuduri da dan Majalisa Garba Datti mai wakiltar Kaduna, da shi da wasu ‘yan majalisu 38 su ka gabatar a yayin zamanta na ranar Talata.
’Yan majalisar sun ce, dalilinsu na gabatar da kudurin shi ne yanayin lalacewar hanyar a yanzu, ya fi karfin na lokacin da aka bayar da kwangilar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, a halin yanzu dai duk lokacin da wata babbar mota ta lalace a kan hanyar matafiya sun shiga uku kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Sarkin Saudiyya ya nada dansa Firayi Ministan kasar
Bayanai sun ce Kamfanin Berger ya kankare tsohuwar kwaltar domin gyara, amma mamakon ruwan sama ya haifar da manyan ramuka da makwantar ruwa da kuma cabi.
Bincike ya nuna cewa, a yanzu dai tafiyar awa daya da rabi zuwa Kaduna, ta zama awa 3 ko ma fiye da haka.
Binciken ya nuna cewa, kamfanin Julius Berger ya janye daga aikin hanyar ne a bisa dalilan tsaro, sakamakon yawan hare-haren ‘yan bindiga da masu sace mutane a kan hanyar.
Sai dai ’yan majalisar sun ce yanzu an inganta tsaro a hanyar, don haka kamfamin ya koma bakin aiki cikin gaggawa.
Majalisar ta umarci Kwamitin Kula da Ayyuka ya hada gwiwa da Mista Fashola da kuma shugabannin hukumomin tsaro don tabbatar da aiwatar da wannan kuduri, sannan ya kawo mata rahoto nan da makonni uku.