KURKURA: Kayan Mayen Da Ya Zama Ruwan-Dare A Tsakanin Al’umma
Daga Mahmud Isa Yola
Kwanan nan, an yi ta samun yaduwar wani kayan maye mai hatsarin gaske wanda aka fi sani da Akuskura/Kurkura ko Akurkura, wanda ake yin shi da Tumfafiya hade da ganyen wiwi da na ‘tobacco’ da wasu sinadarai, wanda kuma ya fi yaduwa a yankin arewaci da kudu maso yammacin Najeriya. Wasu lokutan, Akuskura yana kai mutum ga gargarar mutuwa saboda tsananin karfin sinadaran da aka hada shi da su.
Sunan Akuskura, wanda a wasu lokuta ake kira kuskura ko akurkura, ya samo asali ne daga kalmar “kuskura” na Hausa. Ana amfani da sinadarin Akuskura ne ta hanyar kuskure baki a tofar, ko kuma a shaka a hanci. Da zarar an yi hakan, nan take yake fara aikin sa, inda yake gusar da hankali kai tsaye a mafi yawancin lokuta, da kuma kara kuzarin gabobin jiki, rudar da tunani da hana bacci. A wasu lokutan kuma yakan saka mutum ya shiga cikin mawuyacin hali na tsananin kishi da rikewar makogoro ko suma.
A kwanan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama sama da kwalabe dubu bakwai na haramtacciyar sinadarin a hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda aka aika su zuwa jihohin Borno, Kano, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Gombe da Nasarawa. Duk da cewa wannan shi ne mafi girman kamu da akayi na sinadarin da akayi, akwai da dama da aka kama a wurare mabanbanta kafin shi.
Biyo bayan kamen da aka yi, babban daraktan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC, a wata ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar dake Abuja a ranar 19 ga watan Agusta, ta sanar da hana amfani da sinadarin a hukumance. Ta ce hukumar ta samu rahotanni da dama na amfani da Kurkura musamman a yankin Kudu maso Yamma da Arewacin kasar nan. Daraktan ta kara da cewa ganin hakan ne ya sa hukumar ta shirya taron manema labarai don kara tabbatar wa al’umma haramcin amfani da sinadarin kuskura, sakamakon illolin da take dauke da su.
Akuskura nau’in miyagun kwayoyi ne da ake kira sabbin sinadaran gusar da hankali, a turance (New Psychoactive Substance). NPS sinadarai ne wadanda yarjejeniyar 1961 akan kayan shaye-shaye da Yarjejeniyar 1971 na majalisar dinkin duniya basu ambace su a matsayin kayan shaye-shaye ba saboda a lokacin babu bullar su. Sai dai duk da cewa basa cikin jerin kwayoyi na wadannan yarjejeniya, NPS suna iya daukan illoli ga lafiyar jiki masu tasirin gaske. Wannan yana nuna cewa akuskura ya shiga nau’in miyagun kwayoyi, kamar yanda hukumar NAFDAC ta ayyana
Duk da cewa yana da illoli ga lafiyar dan Adam, kuma yana dauke da sinadaran maye da suka hada da wiwi da sauran su, Akuskura yana yawo a tsakanin masu sayar da maganin gargajiya a garuruwa daban-daban, musamman ma a cikin arewacin Nijeriya a matsayin magani, wanda kuma bincike ya tabbatar da cewa baragurbin kwaya ne.
Masu sayar da shi sukan yi ikirarin cewa yana maganin sanyi, mura, tari, ciwon kai, hawan jini, ciwon suga, karin kuzarin mazantaka, maganin amosani, maganin gajiya da dai sauran su.
A zahirin gaskiya, babu wani ingantaccen nazari da masana sukayi wanda suka samu yakinin cewa Akuskura na maganin ko da daya ne daga cikin wadannan cututtuka. Abun da bincike ya tabbatar shine; kuskura sinadari ne na kwaya wanda hukuma ta haramta amfani da shi.
Wannan kuwa yana nuna cewa duk mai sayar da Kuskura yana taka doka ne kuma zai iya gamuwa da fushin hukuma, haka ma wanda ya ke sha, da wanda yake safarar su, kamar yanda shugaban hukumar NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa ya ayyana a wani hira da yayi da gidan radiyon BBC Hausa, inda yace hukumar NDLEA ba zata saurarawa masu ta’amuli da sinadarin Akuskura ba.