Kotun Ma’aikata ta Kasa ta umarci Qungiyar ASUU ta janye yajin aiki da ta kwashe wata bakwai tana yi.
Da yake yanke hukuncin, Mai shara’a Polycap Hamman ya amince da bukatar Gwamnatin Tarayya na lallai ASUU su koma bakin aikinsu.
Sai dai da yake bayani kan batun, Shugaban ASUU yana mamaki a ce za a tursasa su komawa bakin aiki, inda ya ce kamar a tilasta wa likita ne ya je ya yi wa mara lafiya magani ba tare da son ransa ba.