BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kotu ta daure dalibi wata hudu saboda ya saci indomie

Wata kotu a Gwagwalada a Abuja, a yau Alhamis, ta yanke wa wani ɗalibi, Hilary Yunana, ɗan shekara 19 hukuncin wata huɗu a gidan yari sakamakon satar taliya da kuma indomie a wani kanti.

An tuhumi Yunana, mazaunin ƙauyen Bassa a kan hanyar filin jirgin sama, da laifin karya kofar gida da sata.

Da ya je yanke hukunci, alƙalin kotun, Sani Umar, ya aika Yunana gidan yarin duk da ya amsa laifin sa ya kuma nemi kotun da ta yi masa sassauci.

Sai dai kuma alƙalin ya baiwa matashin zaɓin tarar naira dubu 10 ko kuma ya yi watanni biyu-biyu a kowanne laifi guda biyun.

Alƙalin ya ce hukuncin darasi ne ga duk wani wanda ya ke son bin irin wannan mummunar hanyar.

Tun da fari, mai ƙara, Abdullahi Tanko ya shaida wa kotu cewa mai laifin ya ɓalle shagon wata Gift Ogochukwu da su ke unguwar ɗaya a ranar 4 ga watan Maris.

Ya ce bayan ya fasa shagon, ya sace taliya leda 7 da i domie leda 5 da kuma kuɗi Naira dubu 10, gaba daya dai dubu 13 kenan.

Ya ce laifukan sun sabawa sashe na 346 da 287 na kundin dokar Penal Code kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato.

Leave a Reply