Shugaban kwamitin Hon Bappa Babba Dan-Agundi, ya shaida wa BBC cewa, a fahimtar majalisarsu kwamitin zai ci gaba da gudanar da bincikensa kamar yadda ya tsara don ba cewa aka yi a daina aiki ba.
Bappa Babba Dan Agundi, ya ce kwamitin zai kuma je kotu domin ya girmamata saboda mutanen da ke amajalisar su ne yakamata su kare martaba da mutuncin kotun.
Shugaban kwamitin binciken ya ce, a abinda aka ba su, kotu ba ta ce su daina aikin da suke ba, amma kuma idan har suka je kotun ta kuma ce su daina binciken da suke yi, ai dole su girmama kotu.
Bappa Babba Dan Agundi, ya ce dangane da batun nazarin hotunan bidiyon tare da kwararru da za ayi kuwa, an samu ci gaba tun da an samu wadanda za su zo su bayar da shaida akai.
Dan majlisar dokokin ta jihar Kano, ya ce, dangane da batun ranar da za a kammala nazarin hotuna kuwa, dama a bisa ka’ida ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba yakamata a mika rahoton, don idan ba kotu ce ta tsaida da su ba, zasu iya kammala aikinsu sannan su mika rahoton.