Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

Kame mafi girma: NDLEA ta kama cocaine ta Naira biliyan 193 a Legas

Hukumar NDLEA, ta gano tare da ƙwace kilogiram 1,855 na hodar ibilis da adadin kuɗinta ya kai naira biliyan 194 a wani rumbun ajiya da ke wani gida a Lagos.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, NDLEA ta ce wannan kame shi ne mafi girma da ba a taɓa yin irinsa ba a tarihin ƙwace ƙwayoyi a ƙasar.

An samu muggan ƙwayoyin ne a wani rumbun ajiya da ke wani gini cikin wani rukunin gidaje da ke yankin Ikorodu a cikin birnin Ikkon.

“An kama koken ɗin da darajarsa a kasuwa ta kai dala 278,250,000 wanda ya yi daidai da N194, 775,000,000,” in ji sanarwar kamar yadda BBC ta fassara.

NDLEA ta ce a yayin samamen da aka shirya shi tsaf ta hanyar tattara bayanan sirri da aka shafe kwana biyu ana tattarawa a unguwanni daban-daban na Lagos, an kama wasu manyan dilolin koken huɗu ciki har da wani ɗan ƙasar Jamaica, da kuma manajan gidan ajiyar.

Sanarwar ta ambaci sunayen mutanen da shekaru da ma jihohin da suka fito, kuma ta ce dukkansu suna cikin mambobin ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa da hukumar NDLEA take bibiyarsu tun 2018.

Leave a Reply