Rahotanni da ke zo mana na nuni da cewar Jami’an Tsaron farin kaya na NSCDC reshen Jihar Sokoto, sun yi nasarar chafke wani kasurgumin Ɗan Ta’adda da ya addabi jihar da hare-hare mai suna Alhaji Kwaire.
Ƙwamandan rundunar a Jihar Sakoto, Muhammad Sale Dada, shi ne ya jagoranci aikin kame wannan babban dan ta’addan da ya jima yana kassara al’ummar Jihar da ayyukan ta’addanci.
Duk da yake wanda aka kaman ya ki aminta da cewa shi jagoran barayi ne, amma dai ya ce ya saba amfana da kayan satar.
To sai dai wanda aka kama su tare, Buba, ya ce sun jima cikin wannan Aika-aika.
Accuracy 24