Matar Abdulmalik wanda ake zargi da kashe dalibar makarantarsa Hanifa a Kano ta ce tana so kotu ta sa ya sake ta domin ba za iya zaman jiransa.
Matar ta bayyana hakan ne bayan kotu ta wanke ta tare da sallamarta daga zargin da ake mata na tana da hannu a garkuwa da kashe Hanifa.
Ta bayyana was kotu cewa ita abin da ta sani kawai shi ne mijinta ya kawo mata yarinya ya ce mata yarinyar wata malamar makaransa ce, sannan da ta matsa masa ya dauke ta ya tafi da ita.
Ta kara cewa ita ko labarin bacewar Hanifa da kashe ta ba ta ji ba sai lokacin da jami’an DSS suka gayyace ta.