Bankin Polaris ya nemi afuwa a kan labarin da ake yadawa cewa ya hana ma’aikatansa zuwa Sallar Juma’a.
Kano a Yau ta ruwaito cewa wata manaja a bankin ta hana ma’aikatan da ke karkashinta zuwa Sallar Juma’a.
Sai dai a wata sanarwa da bankin ya fitar, sun CE sun san Najeriya kasa ce mai addinai da dama, don haka ba za su hana kowa yin addininsa ba.
Sanarwar ta kara da cewa wata jami’a ce kawai ta tura wa ma’aikatan da ke karkashinta wannan sako, kuma sun shawo kan lamarin a cikin gida.