Sufeto-Janar na ƴan sanda, Usman Baba, ya ɗora laifin karuwar tashe-tashen hankulan siyasa a kasar kan wasu gwamnonin jihohi.
Baba ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a yau Alhamis a Abuja.
Ya ce an kira taron ne domin jan hankalin shugabannin jam’iyyun siyasa kan yadda ake samun karuwar tashe-tashen hankula a siyasance da kuma gabatar da cikakken tsari na magance matsalolin.
“Muna ta samun rahotannin wasu Gwamnonin Jihohi da ke karfafa ‘yan barandan siyasa.
“Suna amfani da jami’an tsaro na kananan hukumomin da ke karkashinsu domin tada tarzoma a wajen yakin neman zabe na jam’iyyu da aka bada umarni, musamman sabanin ra’ayi na siyasa.
“A yin haka, suna amfani da ikonsu da tasirinsu don hana kafa allunan yakin neman zabe ko kuma su kakkarya su.
“Suna kuma hana ƴan adawar siyasa filaye su gudanar da yakin neman zabensu ko kuma yin taron su na siyasa cikin lumana, wanda hakan ya saɓa wa tanadin dokar zabe ta 2022 (Kamar yadda aka gyara),” in ji shi.
IGP ya ce ya kuma ɗora alhakin mafi yawan tashe-tashen hankula a kan tsattsauran ra’ayi na siyasa, rashin fahimtar juna, rashin hakuri, kuskuren siyasa, kalaman kiyayya, da kuma tunzura jama’a.