A yammacin yau Laraba ne Gwamnatin Najeriya ta bada dalilan ta na sayawa makwabciyarta wato ƙasar Nijar wasu motocin alfarma waɗanda darajar su ta haura Naira biliyan ɗaya, baya ga ita ƙasar Nijar ɗin ta buƙaci ƙasar Najeriyan ta saya mata su don bunƙasa tsaro a ƙasar.
Hakan na zuwa ne baya ga Malaman Jami’a da ke koyarwa a makarantu gwamnatin Najeriya suka shafe sama da wata shida suna gudanar da yajin aiki saboda gaza biya musu buƙata da Gwamnatin Najeriyar ta yi.
Sa take bayyana dalilin tallafin, Ministan Kudi, Zainab Ahmed ta ce dama can Najeriya kan tallafawa makwabtanta musamman a harkokin da suka shafi tsaro domin hakan zai shafi Najeriya kai-tsaye.