Daga Abudu Bulama Bukarti
GODIYA TA MUSAMMAN GA GOVERNOR BUNI AKAN TALLAFAWA IYALAN SHAYKH GONI AISAMI
A madadin iyalan Shaykh Goni Aisami, ina amfani da wannan dama domin mika godiya ta musamman ga Governor Mai Mala Buni akan tallafa wa marayu da matan marigayin Malamin. A yau ne gwamnan ya kar6i bakuncin ‘yan’uwan da almajiran marigayin inda ya:
1. Bayyana musu cewa gwamnatin jaha ta fara daukan matakai domin tabbatar da cewa an hukunta mara sa imanin da suka kashe malamin. Gwamnan ya sanar da Babban Sifeta Janar din ‘Yansanda da Shugaban Sojoji da kuma Fadar Shugaban Kasa cewa iyalan Malan da gwamnatin Yobe ba za su yafe ba. Sannan Gwamna Buni ya bayyana cewa da zarar an yanke wa mara sa imanin hukunci, zai sanya hannu domin a zartar da hukuncin akansu.
2. Gwamna Buni ya bawa ‘ya’yan Malan biyu aikin gwamnati (appointment) domin su tallafa wa iyayensu da kannensu. Tuni Gwamnan ya sanya hannu akan afurubal leta dinsu.
3. Gwamnan yayi alkawarin samar wa iyalan Malan gida domin Malan ya zauna ne a gidan gado. Ya ce ko dai a yiwa gidan da suke zaune kudi, ya biya ko kuma a nemi wani gurin ya saya musu. Gwamna Buni ya ce zai yi wannan ne daga aljihunsa.
4. Gwamna Buni ya sa a kai abinci gidan Malan wanda zai ishe su har su gama takaba.
5. Daga karshe Gwamna Buni yayi alkawarin tallafawa wajen gina wata cibiya wanda Malan ya so ya fara ginawa bana, sannan kuma zai tallafawa karatun ‘ya’yan Malan. Ina ba da shawarar cewa a sakawa wannan cibiya suna Gidauniyar Ustaz Goni Aisami.
Muna godiya ga Gwamna Buni akan abinda ya riga yayi, muna fatan Allah Ya ba shi ikon cika dukkanin alkawurran da dauka, kuma Allah Ya saka masa da mafificin alheri da karrama Shaykh Goni Aisami da yayi.
Audu Bulama Bukarti ne ya wallafa a shafinsa na Facebook