A yau da misalin karfe 5.26 na yamma, a shekara 2024/1446, Maigirma Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sawa sabuwar doka ta sarakuna hannu, bayan yan majalisa a ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore sun gabatar masa da dokar. Wannan doka ta samar da sarakuna masu daraja ta biyu a masarautu uku wanda suka haɗa da Gaya, Karaye da kuma Rano kamar haka:
1. Masarautar Gaya
2. Masarautar Karaye
Karaye da Rogo
3. Masarautar Rano
Rano, Bunkure da Kibiya
Allah Ya tabbatar mana da cigaba, haɗɗin kai da kuma zaman lafiya a Kano.