Hukumar Kula da Inshorar al’umma ta Najeriya NSITF ta shaida wa Majalisar Dattawan Kasar cewa, gara ta cinye takardun da ke kunshe da bayanai kan yadda hukumar ta kashe Naira biliyan 17.158, wanda har yanzu babu duriyarsu.
A shekara ta 2018 ne rahotan binciken kudaden da aka kashe ya bayyana cewa, Asusun na NSITF ya yi amfani da bankunan Skye da First Bank wajen tura Naira biliyan 17.158 zuwa ga asusun bankunan wasu daidaikun mutane da kamfanoni daga watan Janairu zuwa Disambar shekarar 2013.
An dai gaza tantance ainihin makasudin aika makuden kudaden zuwa ga wadannan bankunan na daidaikun mutane da kamfanoni biyo bayan ikirarin NSITF na cewa, gara ta cinye takardun da ke fayyace musabbabin aika kudaden.
Ofishin babban mai binciken kudaden a Najeriya ya gabatar da tambayoyi 50 game da zarge-zargen barnatar da dukiyar kasa da hukumar ta NSITF ta yi, lamarin da yanzu haka ke gaban kwamitinin kula da asusun al’umma na Majalidar Dattawan kasar don ci gaba da bincike.
Kwamitin ya tuhumi tsoffin shugabannin NSITF da suka gabata da kuma na yanzu, amma babu wanda ya iya bada wani gamsasshen bayani, kamar yadda RFI ta ruwaito.
Manaja Darektan NSITF na yanzu, Dr. Michael Akabogu ya bayayna cewa, babu wasu takardu mai nasaba da kudaden da ake bincike a kai da ya tarar a ofishinsa.