BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Farashin kayan abinci ya sauka a Najeriya

Hukumar abinci da ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce farashin kayan abinci ya sauka cikin watanni biyar a jere.

Hukumar ta ce bude hanyoyin fitar da kayan abinci kamar alkama da man girki da daga Ukraine ya taimaka wajen saukar farashin kayan abincin.

Kazalika bunkasa noman alkama a arewacin Amurka ma ya taimaka wajen saukar farashin kayan abincin.

Haka kuma an samu karuwar fitar da kayayyaki daga Australia da kuma Brazil.

Sai dai wasu kwararru sun ce har yanzu akwai damuwa a kan fitar da kayan abincin saboda yanayin da ake ciki na damuna da kuma tsananin zafin da ake fuskanta a wasu kasashen turai da Pakistan ka iya shafar yanayin, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Leave a Reply