BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Fafaroma Benedict ya rasu yana da shekara 95

Faparoma Emeritus Benedict na 16, masanin addinin Kirista dan kasar Jamus, wanda ya yi kokarin farfado da addinin Kirista a cikin kasashen Turai masu hadakar addinai ya mutu.

Ya mutu yana da shekaru 95 a jiya Asabar.

Za a iya tunawa da Fafaroman a matsayin Fafaroma na farko cikin shekaru 600 da ya yi murabus daga aiki.

Ya kasance mutum ne mai kunya.

Sanarwar da mai magana da yawun fadar Vatican Matteo Bruni ya fitar a safiyar jiya Asabar ta ce: “Cikin bakin ciki na sanar da ku cewa Paparoma Emeritus Benedict na 16 ya rasu a yau da karfe 9:34 a gidan ibadar Mater Ecclesia da ke fadar Vatican. Za a fitar da ƙarin bayani da wuri-wuri.”

Fadar Vatican ta ce za a ajiye gawar Benedict ɗin domin mabiya su yi bankwana da ita a ranar Litinin, inda daga bisani binne shi,” Bruni ya shaida wa manema labarai.

Leave a Reply