Hukumar yaƙi da cinhanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika bisa zargin almundahana.
Mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya faɗa wa BBC cewa suna tsare da ministan ne bisa zargin aikata ba daidai ba a lokacin da yake minista.
“Ina tabbatar muku da cewa muna tsare da shi…amma ba zan iya faɗa muku adadin kuɗin da ake zargi ba har sai an kammala bincike,” kamar yadda ya bayyana ta waya.
Wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya na cewa hukumar na zargin Sirika ne da almundahanar kuɗin da suka kai naira tiriliyan takwas.
Hadi Sirika ya riƙe muƙamin ministan sufurin jirgin sama kusan shekara takwas – farko a matsayin ƙaramin minista kafin daga baya ya zama babban minista.
Tsohon ministan ya tayar da ƙura lokacin da ya ƙaddamar da kamfanin sufurin jirgin sama na Nigeria Air ‘yan kwanaki kafin ƙarewar wa’adin gwamnatinsu a watan Mayu, wanda har yanzu bai fara aiki ba