Rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ta Ƙasa, dan majalisar Doguwa da Tudun Wada daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa, yau Talata a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.
Jam’iyyar NNPP ta zargi Doguwa da tada tarzoma biyo bayan ganin rashin nasara a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar, ta kuma zarge shi da ƙona magoya bayanta a ofishinta da ke Tudunwada, tare da harbi da Bindiga.
Wata majiya daga hedkwatar ‘yan sanda ta tabbata wa Daily Trust da kamun, inda ta ce an kama shi ne bisa zargin kisa da ta’addanci wajen jagorantar ‘yan daba zuwa ofishin NNPP tare da kone ofishin da kisan kai.
Kafin a kama shi, ya gana da ‘yan jarida inda ya karyata zargin kisan kai, tare da cewa shi bai taba rike bindiga ba, ballantana ma ya iya harbi.