Manyan Labarai

Dole mu koyi zama da juna lafiya a Filato – Dattawa da matasa

Shugabannin addini da dattawa da matasa sun yi Allah wadai da rikicin baya-bayan nan da ya auku a Jos fadar Jihar Filato, inda suka ce wajibi ne al’ummar jihar su koyi zama da juna lafiya.

Da suke amsa tambayoyin wakilanmu shugabannin da suka hada da Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Kungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir da Shugaban Coci-Cocin Pentecostal na Najeriya (PFN), Rabaran Dangana Steben da Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Jihar Filato Malam Muhammad Nura Abdullahi da kuma Barista Buhari Ibrahim Shehu wani jagoran matasa a garin Jos sun ce babu wani ci gaba da jihar za ta samu a yanayi na tashin hankali.=

Sheikh Sani Jingir ya ce rikicin na Jos babban abin bakin ciki ne, da suke Allah wadai da shi. “Domin mun ga alamun zaman lafiya ya dawo a garin Jos da jihar da kasa baki daya. To amma akwai wadansu mutane, da suka mayar da rikici da kashe-kashen jama’a hanyar cimma mummunar manufarsu.”

Sheikh Jingir ya yi zargin cewa akwai manyan mutanen da suke yin maganganu marasa kyau a kasar nan, inda wani babban tsohon soja a kwanakin baya ya yi kiran wadansu su dauki makamai su kare kansu. “Haka akwai wani tsohon Gwamna da ya yi kira ga mutanen Jihar Filato, su fito su kare kansu. Idan aka ci gaba da zuba ido, wadannan abubuwa suna faruwa za a ci gaba da samun rikice-rikice. Mutane su rika kalaman tayar da hankali a yi masu shiru ba zai kawo gyara ba,” inji shi.

Sheikh Jingir ya koka kan yadda ake tare hanya a yi ta kashe mutane da manufar kazamiyar siyasa ko kabilanci, inda ya ce aika-aikar kashe Janar na soja a jihar a kan hanya ba daidai ba ne. “Babu kasar da za ta ci gaba da irin wadannan abubuwa,” inji shi. Ya ce, babu abin da al’ummar Musulmi suke so in ban da zaman lafiya. Ya ce hatta talakawa Kiristoci ana neman ne sa su a cikin wannan rigama don biyan bukatar wadansu batagarin ’yan siyasa.

Ya yaba wa gwamnatin jihar kan kokarin da take yi wajen tabbatar da zaman lafiya, inda ya bukaci a hukunta duk wanda ke da hannu a tayar da zaune-tsaye komai girmansa. “Duk mutumin da ya fadi muguwar maganar da ta karya tsaro a hukunta shi, amma mutane su je har gidan gwamnati su farfasa motocin gwamnati a kyale su, kamar bai wa mutane dama su rika mayar da hanun agogo baya ne kan nasarorin da Shugaban Kasa ya samu a fannin tsaro a kasar nan,” inji shi.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi Shugaban Coci-Cocin Pentecostal na Najeriya (PFN), Rabaran Dangana Steben ya ce babu al’ummar da za ta samu ci gaba ba tare da zaman lafiya ba. “Ba za a taba samun ci gaba ba tare da zaman lafiya ba, Allah Ya hada Musulmi da Kirista da mabambanta harsuna a Filato da Najeriya, haka Allah Yake so Ya gan mu, don haka ina kira ga mutane su zauna lafiya da juna, wannan kiran ya shafi kowa da kowa ne,” inji shi.

Ya shawarci malaman addini a kullum su rika kira ga matasa Musulmi ko Kirista su fahimci muhimmanci zaman lafiya, kuma ya kamata shugabannin unguwanni su rika jan hankalin matasansu kan muhimmancin zaman lafiya.

“Babu wanda yake so a samu tashin hankali, babu wanda yake da burin idan ya tashi da safe ya rika tunanin bai san me zan faru da rana ba, don haka ya kamata matasa su bude idonsu, kada su yarda a yi amfani da su wajen tayar da zaune-tsaye da sunan addini ko siyasa,” inji shi.

Ya bukaci mutane su rika ba jami’an tsaro hadin kai don su yi aikinsu yadda ya kamata. Ya ce, “Na san gwamnati da jami’an tsaro suna kokari wajen samar da tsaro, amma ina karfafa musu don su kara tashi tsaye domin ganin rikicin bai ta’azzara ba, domin idan rikicin ya ta’azzara za a ci gaba da shiga mawuyacin hali, mutane za su shiga talauci, tattalin arziki zai tabarbare.”

Ba daidai ba ne jama’a su rika kai wa juna hari –Miyetti Allah 

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah reshen Jihar Filato, Malam Muhammad Nura Abdullahi ya shaida wa Aminiya cewa riginmun da suka taso a garin Jos, daga ranar Juma’ar da ta gabata, babu wani mutumin kirki da zai goyi bayansu. “Domin kashe rayukan jama’a da lalata dukiya abu ne mummuna da ya kamata mu yi Allah wadai da shi. Don haka muna shawarta jama’a kowa ya natsu ya zauna da dan uwansa lafiya. Zaman lafiyar nan ya fi komai dadi. Duk lokacin da aka zauna lafiya za ka ga arziki yana shiga cikin jama’a kowa yana walwala yana jin dadin rayuwa. Amma muddin aka ce babu zaman lafiya, za a ci gaba da samun matsaloli hankali kowa a tashe yake,” inji shi.

Ya ce rikicin ya faro ne kamar almara, an sami maganganu daban-daban da ake cewa su ne suka haddasa rikicin. “Wanda ya fi rinjaye a cikin maganganun shi ne an ce wadansu matsafa ne suka yi fada, a tsakaninsu suka kashe junansu daga nan aka samu matsalolin kashe-kashe a Titin Rububa. Daga baya mutane suka harzuka, suka kai wa jami’an tsaro hari suka kone motar soji, inda sojojin suka yi shiri suka yi kan mai uwa da wabi. Daga nan aka fara guje-guje wannan ne ya hargitsa garin” inji shi.

Ya ce shekara17 ke nan ana rikice rikice a Jihar Filato, inda ake kashe-kashe da lalata dukiyar jama’a. Don haka akwai bukatar gwamnati ta yi maganin rikice-rikicen. “Idan gwamnati ta yi adalci ta yi abin da ya dace, wanda ya yi a yi masa wanda ya hakura a taimake shi, a taro jama’a wuri daya a nuna ba dan bora ba dan mowa, za a magance wannan matsala. Misali jami’an rundunar tsaro ta musamman a Jihar Filato, ba ta dauki wani gefe ba, kowa ya yi suna yi masa, kowa ya bari suna girmama shi, wannan shi ne daidai. Amma muddin ba a yi adalci ba, za a ci gaba da samun matsaloli,” inji shi.

Sai ya bukaci al’ummar su yi hakurin zama da juna kuma su kwantar da hankali. “Wadannan kashe-kashe ba za su kai mu ko’ina ba. Ba daidai ba ne a dauko makami ana kai wa juna hari,” inji shi.

Yadda muka hana matasanmu daukar doka a hannu – Barista Shehu

Wani jagoran matasa a garin Jos, Barista Buhari Ibrahim Shehu, ya bayyana wa Aminiya yadda suka yi iyakar kokarinsu wajen hana matasa Musulmi daukar doka a hanunsu a lokacin rikicin.

Barista Buhari wanda ya bayyana rikicin da abin Allah wadai kuma marar dadi ba, ya kare matasa daga zargin haddasa rikicin, wanda kamar an shirya shi ne, sakamakon bacewar Janar Alkali a yankin Du na’yan kabilar Berom. Ya ce tun da aka fara aikin nemo motarsa a yankin aka fara samun cece-ku-ce a garin. “Kuma tsohon Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang, wanda ba matashi ba ne ya fito yana ba da umarni ga mutanensa kan su kare kansu. Wannan magana da ce ta rura rikicin. Ka ga wannan ba laifin matasa ba ne, laifin dattawa ne da ya kamata su tsawatar, amma suke zugawa a dauki makami a yi rikici,” inji shi.

Ya ce a lokacin da rikicin ya tashi, sun yi iyakar kokarinsu wajen hana matasa su dauki doka a hannunsu, suka hana taba wanda ba Musulmi ba a garin Jos. “Domin duk abin da aka yi, ba laifin wanda za su taba ba ne. Wadanda suka hada rigimar suna can gefe suna kallo, wanda ya shigo cikin gari neman abinci ba laifinsa ba ne. Idan ka taba wanda bai san abin da ake yi ba, ba ka yi adalci ba. Don haka muka yi kokarin kwantar wa matasa hankali ta hanyar magana gaba da gaba da kiran waya da kafofin sada zumunta na yanar gizo, muna kiran matasan su kwantar da hankali, a bari gwamnati ta dauki matakin da ya kamata,” inji shi.

Shugaban ya ce idan ana son a magance faruwar rikici a jihar a nan gaba, dole ne gwamnati ta dauki mataki a kan wadanda suke hada rikice-rikicen. Ya ce, “Idan gwamnati ba ta kama wadanda suke hada rikicin tana hukunta su ba, wadannan abubuwa ba za su kare ba. Amma a zo a kama talaka wanda bai san hawa ba bai san sauka ba a kai shi kotu ba daidai ba ne. Domin ba shi ne ya hada rikicin ba.”

Barista Shehu ya tunatar da al’ummar jihar cewa su sani Allah ne Ya halicci Musulmi  da Kirista kuma ya halicci kabilu daban daban, don su zauna tare su amfani juna. “Duk wanda ya dauki makami ya kashe wani, ko ya ji wa wani rauni a ranar Lahira zai zo da jinin mutumin a wuyansa. Don haka mu yi hakuri da juna mu zauna mu fahimci matsalolinmu mu fuskanci yadda za mu magance su,” inji shi.

 

Abin da ya haifar da rikicin na Jos

Aminiya ta gano cewa wani hari da ake zargin ’yan bindiga sun kai wani gida a Hanyar Rukuba da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa, inda aka kashe mutum tara ’yan gida daya ne ya zamo ummulhaba’isin tashin rikicin na baya-bayan nan a Jos.

Al’amarin ya faru da dare ne a ranar Alhamis din makon bayan ’yan bindigar sun shiga wani gida a kusa da otel din Kowa Hotel, inda aka yi zargin sun yi kisan.

Washegari Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, ta bakin Kakakinta Tyopeb Terna ta ce maharan ’yan bindiga ne da ba san ko su wane ne ba, duk da unguwar ta sha fama da rikicin ’yan kungiyar asiri.

A ranar Juma’ar da ta gabata sai matasan Hanyar Rukuba wadanda akasari Kirista ne suka tare hanya suka fara zanga-zanga, inda suka jikkata wani mai tuka Keke-NAPEP Musulmi. Wannan ne ya sanya matasan Musulmi su ma suka nemi daukar fansa.

Wakilin Aminiya ya iske dandanzon matasa Musulmi da Kirista sun cirko-cirko a shatale-talen da ke Asibitin Ola Hospital, suna shirin far wa juna, sai dai kafin su kai ga haka ne,  jami’an Runduna ta Musamman ta samar da zaman lafiya a Jihar Filato (OPSH) suka watsa su.

Haka aka yi Sallar Juma’a cikin dar-dar, daga bisani Gwamnatin Jihar ta kafa dokar takaita zirga-zirga daga karfe 6:00 a safe zuwa 6:00 na yamma.

Wannan mataki ya sanya washegari Asabar jama’a suka ci gaba da gudanar da harkokinsu, sai dai a ranar Lahadin da ta gabata sai garin Jos ya sake yamutsewa bayan an samu rahoton cewa wadansu matasa Kiristoci sun kashe wani mai acaba a mahadar Tina Junction da ke kusa da Celebridge a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Aminiya ta ji cewa matasan sun far wa dan acabar ne lokacin da yake kokarin wucewa zuwa wata mahada da ake kira British America Junction.

Kisan ne ya sanya matasa Musulmi a Unguwar Dutse uku, suka fara zanga-zanga tare da yunkurin daukar fansa.

Wani da lamarin ya faru a idonsa mai suna Mohammed Dahiru ya bayyana wa Aminiya cewa ba don shugabannin al’umma da na matasa su dauki mataki da wuri ba da tun a safiyar ranar Lahadin rikici zai barke.Ya ce, “A lokacin da mutane suka fahimci an kashe dan acabar sai matasa suka nemi daukar fansa, hakan ya sa mutane suka fara guje-guje, amma komai ya lafa bayan matasa da shugabannin unguwa sun tashi tsaye.”

Daga nan sai aka sake jin barkewar rikici, inda aka fara jin harbe-harbe a Dutse Uku da Unguwar Damusa da Katako Junction da Rikkos da Unguwar Rukuba da Jami’ar Jos da kuma Laranto.

Kuma an rika jita-jitar cewa an kashe daliban Jami’ar Jos bakwai a rikicin, amma Kakakin Jami’ar, Abdullahi Abdullahi ya musanta haka, inda ya tabbatar da mutuwar dalibi daya, kuma daya da ya bace an same shi a ranar Talata.

Z uwa hada wannan rahoto ba a san adadin mutanen da suka rasu, ko adadin gidajen da aka kone ballantana wadanda suka samu raunuka ba, saboda hukumomin tsaro da gwamnti sun ki su bayyana hakan.

A lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, Tyopeb Terna ya tabbatar aukuwar rikicin, inda ya ce, “Jiya (Alhamis, 27 ga Satumba, 2018), da misalin karfe 10 na dare mun samu rahoto harbe-harben bindiga a Hanyar Rukuba Road daura da Kowa Hotel, hakan ya sa muka tura jami’anmu wurin. Jami’anmu da na Rundunar OPSH sun fatattaki ’yan bindigar, kuma sakamakon harin wadansu sun rasu, wadansu sun samu raunuka, inda aka kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bingham,” inji shi.

 

Leave a Reply