An dai sace shi ne tun lokacin da mahara suka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari, sannan suka sace mutane da dama.
Sadiq dai ya sami kuri’a 28 yayin da sauran ’yan takarar suka biyo baya.
Sauran ’yan takarar, Hadiza Muhammad, da kuma Misis Paulina, Salisu Abdulhamud suka sha kaye a zaben kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Idan za a iya tunawa tun a ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2022 ’yan bindigar suka yi awon gaba da shi da wasu matafiya a jirgin kasa.
Tun a lokacin ba a sake jin duriyarsa ba a fagen siyasan ba.