Mahukunta a kasar China sun kama wani matsahi dan shekara 17 wanda ya yi watsi da karatunsa a makarantar sakandare yake ta yada kansa a kafafen sadarwar zamani da nufin yaudarar jama’a tare hada hotunansa da hotunan wadansu shugabannin kasashen waje a matsayin shi attajiri ne.
Jami’an ’yan sandan Lardin Shandong da ke Arewacin China sun ce suna ci gaba da binciken matashin wanda ke amfani da sunan mahaifinsa wato Shi, yana kuma gabatar da kansa a shafukan sadarwar zamani da sunan Sh Runlong Jocker, yayin da yake yi wa kansa lakabi da cewa shi ne attajirin kasar China daga Hong Kong.
Shi, yana yada labaran karya yana bayyana ko shi wane ne, a cikin bayanan da yake yadawa akwai batun cewa, shi mamba ne kungiyar Red Cross ta Japan kuma yana rike da mukamin Darakta a cibiyar binciken tattalin arziki ta Shandong ya kuma yada hotunansa na bogi da ya dauka da Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel.
An dai taba zargin Shi, da yada wata kasida a kafar labarai ta Dinhua news wanda daga bisani aka gano labaran na karya ne, rubutun na bayyana cewa, Shi ya shahara a fannin magance talauci.
Matashin dai ya kasance yana biyan mutane don yada labaran karya tare da sanya hotunan karya a shafukan sadarwa na zamani. Sai dai jami’an tsaron Lardin Shandong sun ce sun dauki matakin hukunta masu yada labarai da hotunan karya a shafukan sadarwa na zamani a fallen Weibo.
Shafin Shi a kafar sadarwar zamani ya shahara, inda shafin sadarwarsa na Twitter yake da mabiya da suka kai sama da mutum 10,000. Sai dai a shekaranjiya Laraba kafar labarai ta Reuters ta ce ba ta iya bude shafin ba.