Dan Takarar shugaban Najeriya a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sha alwashin mikawa gwamnatocin jihohi manyan jami’oin tarayya da zarar an zabe shi shugaban kasar a shekara mai zuwa.
Atiku ya shaidawa taron kungiyar lauyoyin kasar cewa daya daga cikin manufofin da ya tsara zai aiwatar idan an zabe shi, shine sakin mara ga bangaren yan kasuwa wadanda suke cikin gida da kasashen ketare, saboda gwamnatin tarayya bata da kudaden gudanar da kowanne aiki.
Tsohon mataimakin shugaban kasar yace gwamnatin sa zata samar da yanayi mai kyau wanda zai baiwa masu zuba jari damar taka rawa a bangaren ilimi da gina kayan more rayuwa da kuma bangaren kula da lafiya.
Dangane da halin da Najeriya ke ciki a wannan lokaci kuwa, Atiku yace Najeriya bata taba shiga cikin irin wannan mummunar yanayi na talauci da rashin tsaro da kuma rashin aikin yi ba, tun daga shekarar 1999 irin na wannan lokaci.
Dan takaran shugaban kasar yace Najeriya a yau ta fice daga hayyacinta ta kowacce fuska, abinda ya kai ga rarraba kan jama’ar kasar, dalilin da ya sa take bukatar kwararre domin dawo da ita cikin hayyacinta.