Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon tsari kan yawan jama’a don ci gaba mai dorewa a Najeriya.
Shugaban ya ƙaddamar da wannan shiri ne a fadarsa da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Shugaban ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan ƙaruwar da ake samu na haihuwa ta hanyar faɗaɗa shirye-shiryen samar da hanyoyin bayar da tazarar haihuwa na zamani a faɗin ƙasar.
Domin tabbatar da wannan tsarin, shugaban ya kafa wani kwamiti da zai riƙa sa ido kan yawan jama’a wanda shi da kansa zai jagoranta, sai kuma mataimakinsa zai ci gaba da taimaka masa a wannan ɓangare haka kuma akwai shugabannin wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnatin a matsayin mambobi.
Shugaba Buhari ya ce babban burin wannan shiri shi ne inganta rayuwar duka yan Najeriya wanda hakan na daga cikin abin da gwamnatin ƙasar ke son cimmawa.
Buhari ya ce ƴan Najeriya sun fi kowace al’umma yawa a nahiyar Afrika kuma ita ce ta bakwai a duniya baki ɗaya kuma tana daga cikin ƙasashe ƙalilan na duniya da ake ƙara samun haihuwa sosai – ƙasar ta dogara kan matasa inda sama da kashi 72 cikin 100 na matasan na ƙasa da shekara 30 inda rabin matan ƙasar na cikin shekarunsu na haihuwa wato tsakanin shekara 15 zuwa 49, kama yadda muka kalato daga BBC.