Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Aliko Dangote, Aminu Dantata da Abdussamad Isyaku Rabiu a matsayin mambobi na kwamitin gudanarwa na Hukumar Zakka da Hubusi ta Kano.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.
Garba ya ce Dakta Ibrahim Muazzam Maibushira, shi ne a ka naɗa a matsayin Shugaban kwamitin.
Sauran, a cewar Kwamishinan, sun haɗa da Dakta AbdulMutallab Ahmed a matsayin Kwamishina I sai kuma Dakta Lawi Sheikh Atiq a matsayin Kwamishina na ll a hukumar.
Sauran sun haɗa da wakilan Masarautar Kano, wakilan Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Wakilan Ma’aikatar Harkokin Addinai, sai na kasuwannin kurmi, Rimi, Kwari da Singa kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.