Wani ɗalibi ɗan ƙasar Nijar ya rasu a hanyar komawa gida daga Sudan bayan an kwaso su yayin da ake ci gaba da gwaɓza faɗa tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF.
Ɗaya daga cikin wakilan ɗaliban, Ahmad Rabe Kani, ya ce ɗalibin ya rasu ne a kan hanya kafin su isa gida.
Ya ce sun bar Sudan cikin ƙoshin lafiya tare da ɗalibin, amma da zuwansu Chadi sai ya yanke jiki ya faɗi.
Ya ce a yanzu an isa Yamai da gawar ɗalibin domin yi masa jana’iza, kamar yadda BBC ta kalato.
Ɗaliban Nijar ɗin dai sun shafe tsawon kwanaki a Port Sudan kafin daga bisani su isa zuwa N’djamena da kuma komawa ƙasarsu ta wani jirgin soji.
Ya ce su ɗaliban sun kai 45, inda ya ce akwai sauran mutum takwas a birnin Port Sudan.