A Juma’ar nan ce wani rahoto ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga a motoci uku sun yi harbe-harbe da misalin karfe 12:30 na rana a hedikwatar ‘yan sandan ta Zone 1, inda daga bisani suka tsere daga wurin, lamarin da majiyar ‘yan sandan ta musanta cewa babu wani hari ko yunkurin kai hari da aka kai musu.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar ya karyata labarin, sai dai Jaridar Daily Nigerian ta ce tana kan bakanta kan lamarin.
Binciken Kano a Yau ya gano cewa mutane da yawa sun musanta labarin.
Sai dai biyo bayan samun labarin, an tsaurara matakan tsaro a cikin garin na Kano.