BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ciyaman ɗin NNPP na kasa, Farfesa Alkali ya yi murabus

Shugaban jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na kasa, Farfesa Ahmed Alkali ya yi murabus.

Jam’iyyar NNPP da dan takararta na shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ce su ka zo na hudu a zaben shugaban kasa da aka kammala kwanan nan, inda ta kuma lashe zaben gwamnan Kano.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 31 ga Maris, 2023 ya kuma aikewa da sakataren jam’iyar na kasa, Farfesa Alkali ya ce ya ajiye mukaminsa na shugabancin jam’iyyar na kasa ne domin bada damar sake fasalin jam’iyyar tare da cicciɓa ta ta samu nasarori nan gaba, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato.

Wasikar murabus din na zuwa ne sa’o’i 24 da kammala taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar na kasa.

Ya kuma aike da kwafin wasikar zuwa ga dan takarar shugaban kasa kuma jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da shugaban kwamitin amintattu, dattijo Cif Boniface Aniebonam, da sakataren kwamitin amintattu, Engr. Buba Galadima.

Ya ce akwai bukatar shugabannin jam’iyyar su yi sadaukarwa don ganin an sake sauya fasalin jam’iyyar domin samun damar lashe dukkanin zabukan da za a yi nan gaba, yana mai cewa ya kamata sadaukarwar ta fara daga kan sa.

Leave a Reply