Karon farko tun bayan zaben gwamnoni a Najeriya, fadar shugaban kasa ta bara game da zaben jihar Kano mai cike da takaddama.
Dumbin mutane da kungiyoyi, sun yi ta bayyana ra’ayoyi daban-daban kan sakamakon zaben gwamnan na Kano, inda wasu suka kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yin shiru ga zarge-zargen amfani da ‘yan daba da tarzoma musamman a zaben cike-gibin da aka yi.
Wata kungiyar matasan jam’iyyar APC ta Muhammadu Buhari ma ta fito tana kira ga uwar jam’iyyar a kan ta gudanar da bincike da nufin hukunta masu hannu cikin abubuwan da suka faru.
Malam Garba Shehu, shi ne mai magana da yawun shugaba Buhari, ga kuma karin bayanin da ya yi wa Yusuf Ibrahim Yakasai a wata hirar da suka yi kan batun kamar yadda BBC ta rawaito.