Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ƴan Najeriya ba su da wani dalili na yin kuka a kan yunwa a lokacin da kasar ke da albarkacin katafarun filayen noma.
Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin naTambari Hausa TV, wacce aka watsa a daren Laraba.
A yayin da ya ke amsa tambaya kan yadda ake fama da yunwa a kasar, shugaban ya ce duk wanda da gaske yunwar ya ke ji to kuwa zai ɗauki kayan Noma ya nufi gona.
A cewarsa, rufe iyakokin kasa da sauran manufofin da gwamnatinsa ta bullo da su don tabbatar da samar da abinci ya haifar da sakamako mai kyau.
“Idan ku na kokarin ku kai rahoto na ga ƴan Nijeriya cewa ban cika alkawari na ba, bari in tambaye ku, lokacin da na hau mulki, ban ba da umarnin rufe iyakokin kasa ba har kusan shekaru biyu?” .
“Na dauki wannan matakin ne na dakatar da shigo da shinkafa daga kasashen waje, na ce mu noma abin da muke ci ko kuma mu mutu da yunwa.
“Na ce tunda mu na da filin noma kuma Allah Ya albarkace mu da ruwan sama, wane dalili ne dan Nijeriya zai ce yana fama da yunwa? In kana jin yunwa ka tafi gona.”in ji Buhari kamar yadda muka kalato daga Daily Nigerian Hausa.