BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ba mu haramta shan giya ba -Gwamnan Neja

Gwamnan Neja, Umaru Bago ya karyata labarin da ke yawo cewa gwamnatinsa ta haramta giya a jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito Gwamna Bago yana cewa babu kamshin gaskiya a labarin, domin kuwa, daga shi har jami’an gwamnatinsa babu wanda ya bayar da umarnin haramta giya a jihar.

A sanarwa da Bago ya fitar a Abuja ranar Alhamis, ya bukaci “jama’a su yi watsi da rahoton da ke yawo a kafofin sada zumunta, cewa Gwamnatin Jihar Neja ta haramta sayar da giya.”

Ya kara da cewa, “Labarin kanzon kuregen na cewa Hukumar Bayar da Lasisin Barasa ta jihar ce ta haramta shan giya a wasu kananan hukumomi tara, ciki har da Suleja.

“Muna so jama’a su sani cewa gwamnan bai taba bayar da irin wannan umarnin ba, ya shagaltu ne da assasawa da kuma lura da ayyuka da suka shafi jama’a a fadin jihar.

“Haka kuma, babu wata Hukumar Bayar da Lasisin Barasa da gwamna ya karkira, don haka babu yadda za a yi wani umarni ya fito daga hukumar da babu ita.”

Sanarwar ta ce Bago ya umurci jami’an tsaro da su kamo sakataren hukumar bogin da ya nada kansa mai suna Mohammed Ibrahim.

Ya ce dole ne a gano manufar mutumin da kuma dalilan da suka sa ya fitar da sanarwar.

“Muna kira ga jama’a da kafofin yada labarai da su yi watsi da umarnin, sannan su rika neman karin haske daga sanannun jami’an gwamnati,” in ji shi.

Leave a Reply